Yadda aka yi walimar karrama Tinubu a masarautar Birtaniya

Asalin hoton, PA Media
- Marubuci, Sean Coughlan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Royal correspondent
- Lokacin karatu: Minti 4
Sarki Charles ya tarbi shugaban Najeriya da matarsa a wata ƙwarya-ƙwaryar walima, inda ya jinjinawa Najriya saboda kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ta da Birtaniya.
Bayan gaisuwa da harshen Yarbanci da ya yi wa baƙi 160 da suka halarci walimar, sarkin yabi al'ummar Najeriya mazauna Birtaniya.
Taron walima ya gudana ne a ɗakin taro na St George a fadar Windsor.
Manyan baƙi da suka halarta harda wakilcin rukunnan gidan sarautar Birtaniya.
An yi tsari na musamman ta yadda walimar za ta yi daidai da yanayin da ake ciki na azumin watan Ramadan domin al'ummar musulmai da suka halarta.

Asalin hoton, PA Media

Asalin hoton, PA Media
Yayin wannan walima an soke wani taron addu'a da ya zamo al'adar irin wannan ziyara a baya, inda sarki ke jagorantar adu'oin a fadar Winsor.
An kuma sauya al'adar rabon kayayyakin sha a yayin ziyarar inda aka maye gurbin barasa da lemun zoɓo ɗan Najeriya da kuma wani lemun da aka yi da cita.
Jawabin sarkin ya yi tsokaci ne a kan muhimmancin zaman tare da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai mabanbanta, waɗanda ya ce dole ne mutane su fahimci fa'idar zaman lafiya da juna domin ci gaban kowa.
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗaka tsakanin ƙasashe, irin wadda ake samu tsakanin Najeriya da Birtaniya, domin tallafawa juna a lokacin buƙata.
Sarki Charles ya kuma bayyana Najeriya a matsayin ''jigo a fannin alaƙar bunƙasa tatalin arziki da bunƙasa al'adu da kuma inganta hudɗar diflomasiyya.''
"Ina fatan cimma gagarumar nasara tare da junanmu, ta yadda waɗanda suka assasa wannan alaƙa za su ji daɗin inda ta kai mu.'' in ji sarki Charles.

Asalin hoton, PA Media

Asalin hoton, PA Media

Asalin hoton, PA Media
An fara ziyarar kwana biyu ta shugaba Tinubu a Najeriya ne da ƙwarya-ƙwayan biki a fadar Windsor.
Shugaban ƙasar tare da matarsa sun bayyana sanye da kayan gargajiya na Najeriya inda aka yi masu faretin ban girma.
An kuma zagaya da shugaban Najeriyan zuwa sassan fadar sarkin Birtaniya, inda aka riƙa yi mashi fareti da jinjina.
Akwai kuma sauraron taken ƙasashen biyu da zagayen sojoji cikin ɗamara, kamar dai yadda fadar ta saba yi wa baƙin ta.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Getty Images
An yi musayar kyautuka, inda aka bai wa Mrs Tinubu wata tukunyar gargajiya da wani babban hoto na sarki da sarauniya.
Su kuma sarki da sarauniya an basu kyautar kayan al'adar Yarbawa da wani ɗan akwati ɗauke da sarƙoƙi da aka yi wa kwalliya da hotunan muhimman matan Najeriya.
Shugaba Tinubu Musulmi ne kuma matarsa kirista ce, kuma dukkansu sun halarci wani taron mabiya addinai daban-daban a fadar Windsor da nufin ƙulla alaƙa mai ƙarfi tsakanin addinai.
Wannan ne karon farko da wani shugaban Najeriya ya kai irin wannan ziyara Birtaniya a tsawon shekaru 37.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Sign up here to get the latest royal stories and analysis every week with our Royal Watch newsletter. Those outside the UK can sign up here.











