Wane tasiri yanayin zafi ke yi wa ƙwaƙwalwarmu?

    • Marubuci, Theres Lüthi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • Lokacin karatu: Minti 7

Lokacin da Jake yake wata biyar ne ya fara gamuwa da matsalar jijjiga da ke sa gabobin mutum su kandare ba a saurin tankwasa su.

"Ana matsanancin zafi lokacin, a don haka jikinsa ya yi zafi sosai, lamarin da ya sa ya yi fama da wannan matsala da muka yi tunanin shi ne abu mafi razanarwa da muka taba gani. In ji.

Mahaifiyarsa, Stephanie Smith. "Sai dai abin ba haka ya kasance ba."

Matsalar farfadiya da ke shafar kwakwalwa ta fara zuwa ba zato ba tsammani, galibi a lokutan zafi.

Da zarar aka shiga lokacin bazara, sai iyalin su shiga neman hanyoyin sanyaya gida da fafutukar sun kare dan nasu daga fama da farfadiyar.

Bayan wani gwajin halittar gado da aka yi masa yana wata 18 da haihuwa, an gano Jake na dauke da wata matsalar kwakwalwa da ke zuwa da farfadiya mai suna Dravet Syndrome wadda kuma take shafar kusan yaro daya cikin 15,000.

Farfaɗiya galibi na zuwa da matsalar kwakwalwa da wasu matsalolin kamar larurar kwakwalwa ta autism da lalurar tsananin rashin mayar da hankali ta ADHD da kuma rashin iya magana da motsa jiki da cin abinci da barci.

Zafi da sauye-sauyen yanayi na iya haifar da farfadiya.

Yanzu shekarar Jake 13 amma ya yi fama da farfadiya lokuta da dama sakamakon sauyawar yanayi, in ji mahaifiyarsa.

"Karuwar yanayin zafi na kara haifar wa masu fama da wannan larura mai matukar karya zuciya matsala," in ji Smith.

Dravet Syndrome daya ce daga cikin matsalolin kwakwalwa da yanayin zafi ke ingiza su, in ji Sanjay Sisodiya na Jami'ar College London kuma wanda ke nazari kan tasirin sauyin yanayi a kan kwakwalwa.

A matsayinsa na ikitan kwakwalwa da ya kware a fannin farfadiya, yana yawan ji daga iyalan masu fama da larurar cewa matsalarsu ta fi tashi a lokutan zafi.

"Sai na yi tunani, me ya sa sauyin yanayi ba zai shafi kwakwalwa ba? Saboda akwai abubuwa da dama da ke wakana a cikin kwakwalwa da suka shafi yadda jikin bil adama ke jure wa yanayin zafi."

Da ya zurfafa bincike, ya gano wasu matsaloli da suka shafi kwakwalwa da suke tsananta sakamakon karuwar yanayin zafi ciki har da farfadiya da bugun jini da matsalar kwakwalwa ta encephalitis da cutar sclerosis da ta shafi jijiyoyi da ciwon kai na bari guda da sauran wasu matsalolin.

Ya kuma gano cewa tasirin sauyin yanayi kan kwakwalwar bil adama abu ne da tuni ke fitowa fili.

Lokacin da aka yi fama da matsanancin zafi a Turai a 2003, misali, kusan kashi 7 cikin 100 na mace-macen da aka yi suna da nasaba da matsalolin kwakwalwa.

An kuma ga makamancin alkaluman a matsanancin zafin da aka yi a Birtaniya cikin 2022.

Sai dai zafi na iya shafar wasu hanyoyin da kwakwalwarmu ke aiki - abin da ke kara sa mu zama cikin bacin rai ko damuwa ko mu zama masu saurin fusata.

Don haka yayin da duniya ke dumama saboda sauyin yanayi, wane irin tasiri muke tunanin hakan zai yi ga kwakwalwarmu?

Kwakwalwar bil adama, a matsakaicin lokaci, bai cika zarce maki 1 a ma'aunin salshiyos fiye da zafin jikinmu ba.

Duk da haka kwakwalwarmu - a matsayin daya daga cikin gabobinmu da ke yawan amfani da kuzari - na fitar da wani kaso na zafi idan muna tunani ko muka tuna wani abin.

Hakan na nufin dole ne jikinmu ya yi aiki tukuru domin sanyaya ta. Jinin da ke zagayawa ta hanyoyin jini na taimakawa wajen daidaita yanayin zafi tare da kore zafi mai yawa.

Hakan ya zama dole saboda sinadaran da ke kwakwalwarmu suna fitar da zafi sosai.

Kuma amfanin wasu daga cikin kwayoyin halittar da ke isar da sako a tsakaninsu suma sun dogara kan zafi, ma'ana suna daina aiki yadda ya kamata idan kwakwalwarmu ta cika zafi ko ta cika sanyi.

"Ba mu gama fahimtar yadda lamarin ke shafar wadannan halittu daban-daban ba," in ji Sisodiya.

"Amma muna iya hararo lamarin a matsayin agogo, inda kowane bangare na jikinsa suka daina aiki tare yadda ya kamata."

Duk da cewa matsanancin yanayin zafi na iya sauya yadda kwakwalwar kowa ke aiki - za ta iya, misali, shafar yanayin daukar mataki tare da jefa mutane su dauki wata matsaya mai hadari - waɗanda suke da matsalolin kwakwalwa su lamarin ya fi wa illa.

Wannan saboda dalilai masu yawa.

Misali, a wasu cututtukan, gumi na iya samun matsala.

"Iya daidaita yanayin dumi wani aiki ne na kwakwalwa kuma hakan na iya fuskantar cikas, idan wasu bangarorin kwakwalwa suna da matsala ba sa aiki yadda ya kamata," in ji Sisodiya.

A wasu matsalolin jijiyoyi kamar a cutar sclerosis, misali, yanayin dumin jiki na iya sauyawa.

Sannan wasu magungunan da ake bai wa masu matsalolin kwakwalwa kamar ta gushewar hankali wato schizophrenia na shafar yanayin daidaituwar zafi abin da ke sa wadandake shan su su kasance masu hadarin fuskantar matsanancin zafin jiki da kuma hadarin rasa rayuwarsu saboda zafi.

Matsanancin zafi - da karuwarsa a lokacin kwanciya - na iya shafar yadda mutane ke barci, da sauya yanayin mutum har ma ya ta'azzara alamomin wasu matsalolin.

"Ga mutane da dama da ke fama da farfadiya, rashin kwanciya na kara hadarin jijjiga," in ji Sisodiya.

Hujjoji sun bayyana cewa adadin mutanen da ake kwantarwa a asibiti ko ma suke mutuwa tsakanin masu fama da cutar mantuwa na karuwa a lokacin da ake fama da tsananin zafi.

Wani bangare na hakan na iya kasancewa saboda shekarunsu - mutanen da shekarunsu suka ja ba sa iya daidaita dumin jikinsu - amma matsalar da ta shafi tunaninsu na iya zama ba sa iya jurewa yanayi na matsanancin zafi.

Ba lalle su iya shan isasshen ruwa ba, misali, ko ma su manta su rufe taga, ko ma su fita cikin zafi lokacin da bai kamata su fita ba.

Karuwar yanayin zafi na da nasaba da karuwar bugun jini ko mace-mace. A wani bincike da aka yi wanda ya yi nazari kan mace-mace sakamakon bugun jini daga kasashe 25, masu binciken sun gano cewa cikin mace-mace 1,000 da aka samu daga matsalar toshewar jijiyoyin jini ta schemic stroke, ranakun da aka yi matsanancin zafi ya kara haifar da asarar rayuka.

"Hakan na iya zama da yawa," in ji Bethan Davies, masaniya kan lafiyar tsofaffi a Jami'ar koyarwa ta Sussex da ke Birtaniya.

"Sai dai ganin cewa akwai mutum miliyan bakwai da suke mutuwa sakamakon bugun jini duk shekara a duniya, zafi na iya janyo karin mace-mace fiye da 10,000 ta sanadin bugun jini duk shekara."

Ita da abokan aikinta sun yi gargadi cewa sauyin yanayi na iya haifar da hakan a shekaru masu zuwa.

Wani kaso na mutanen da za su yi fama da bugun jini sakamakon yanayin zafi zai kasance a tsakanin kasashe matalauta da masu matsakaicin arziki, wadanda tuni sauyin yanayi ke yi wa tasiri kuma suke fuskantar adadi mafi yawa na masu fama da matsalar bugun jini.

"Karuwar yanyin zafi na haifar da matsalolin lafiya tsakanin kasashe da mutane," in ji Davies.

Binciken da aka sha yi ya nuna cewa mutanen da shekarunsu suka ja da kuma wadanda ke da matsakaicin arziki na daga cikin wadanda suka fi fuskantar hadarin mutuwa ta sanadin matsalolin zafi.

Yanayin zafi na shafar yadda kwakwarwar kananan yara ke bunkasa. "Akwai alaka tsakanin tsananin zafi da kuma matsalolin haihuwa kamar haihuwar bakwaini," in ji Jane Hirst, farfesa a bangaren lafiyar mata da ke Imperial College a London.

Wani nazari da aka yi a baya-bayan nan ya gano cewa matsanancin zafi na da alaka da kashi 26 cikin 100 na bakwaini da ake haifa, lamarin da ka iya shafar ginubuwar kwakwalwar yaro.

"Sai dai, akwai abubuwa da dama da ba mu sani ba," in ji Hirst.

"Wane ya fi rauni kuma mene ne dalili? Saboda a zahiri, akwai mata miliyan 130 da ke haihuwa kowane shekara, mafi yawansu a kasashe masu fama da yanayin zafi, kuma hakan ba ya faruwa da su."

Matsanancin zafi saboda sauyin yanayi na iya haifar wa kwakwalwa matsala, har ta kai ga tana cikin hadari da ka iya haifar da cututtukan kwakwalwa.

Zafi na iya shafar kariyar da ke kare kwakwalwa, ya sa ta zama mai rauni ta yadda kwayoyin cuta da na iya tsallakawa ga kwakwalwar.

Hakan na iya zama mai muhimmanci yayin da yanyin zafi ke karuwa, haka kuma za a samu karuwar sauro da ke saka kwayoyin cutar da ke haifar da cutar kwakwalwa kamar Zika da chikungunya da zazzabin dengue.

"Kwayar cutar Zika na iya shafar dan tayi ta kuma sa a haifi yaro mai karamin kai da ake kira microcephaly," in ji Tobias Suter, wani likitan kwari da ke cibiyar Swiss Tropical and Public Health.

"Karuwar yanayin zafi da yanayin sanyi na nufin lokacin da sauro ke hayayyafa zai soma da wuri a shekara ya kuma kare daga baya."

Yanayin matsanancin zafi na iya shafar abubuwa da dama sai dai yadda karuwar yanayin ke iya shafar kwakwalwa ne har yanzu masana kimiyya ke gudanar da bincike a kai.

Zafi na shafar mutum ta hanyoyi daban-daban - wasu sun fi kuzari a lokacin zafi, wasu kuma sam ba sa sakewa.

"Abubuwa daban-daban na iya zama da muhimmanci kan abin da ke sa a samu wadannen bambance-bambance kuma daya daga cikinsu na iya kasancewa yana da alaka da gado, in ji Sisodiya.

Bambancin halittun gado na iya yin tasiri a yanayin sinadarin protein da ka iya sa wasu su fi rauni idan ana batun tasirin sauyin yanayi.

Akwai tarin tambayoyi da har yanzu ba a amsa ba.

Misali, shin ya danganci matsanancin yanayi ne ko kuma tsawon lokacin da yanayin zafin ya dauka ko kuma yanayin lokacin barci ne ya fi tasiri?

Hakan na iya bambanta tsakanin mutane ko kuma yanayin kwakwalwa.

Amma gano wanda yake cikin hadari da kuma dalilin na da muhimmanci wajen samar da dabaru na kare wadanda suka fi rauni.

Hakan na iya shafar tsarin gargadi ko inshora don sakawa masu aiki a rana saboda tsananin zafi.

"Zamanin dumamar yanayi ya zo karshe, zamanin tururin zafi ya iso," in ji Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres lokacin da aka ayyana Yulin 2023 a matsayin wata mafi zafi da aka taba yi a tarihi.

Sauyin yanayi ya zo kuma yana ta'azzara. Yanzu zamanin dumamar kwakwalwa ke somawa.