Wane ne Chukwunyere Nwabuoko da kotu ta ɗaure shekaru 72?

Lokacin karatu: Minti 2

A ranar Litinin ɗin nan ne dai hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa, EFCC ta sanar da cewa an yanke wa tsohon Akanta janar na Najeriya, Chukwunyere Anamekwe Nwabuoko hukuncin zaman gidan yari na shekara 72, bisa samun shi da laifin almundahanar kuɗi da suka kai yawan naira miliyan 868.46.

A shafinta na X, EFCC ta ce babbar kotun tarayya a Abuja ce ta yanke masa hukuncin.

An dai naɗa Nwabuoku a matsayin muƙaddashin Akanta Janar na Najeriya a watan Mayun 2022 bayan dakatar da Ahmed Idris bisa zargin almundahana ta tsabar kuɗi har naira miliyan 800.

EFCC ce ta gabatar da Nwabuoku a gaban kuliya a ranar 15 ga watan Janairun 2025 bisa tuhume-tuhume masu alaƙa da laifuka guda 9, kafin daga bisani alƙali ya bayar da belinsa a kan kuɗi naira miliyan 500 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa.

Yadda kotu ta sami Nwabuoku da laifi

Da yake yanke hukunci, alƙalin kotun James Omotosho ya ce hukumar EFCC ta gabatar da dukkan shaidun da ake buƙata, inda kotun ta same da aikata laifuka 9:

Kotun ta ce Nwabuoku ya karkatar da kuɗaɗen da aka tabbatar haramtattu ne bisa haɗin gwiwar Temero Synergy Concept Limited da Turge Global Investment Limited da Laptev Bridge Limited da kuma Arafura Transnational Afro Limited

Bisa doka, laifin ya saɓa sashe na 18 na dokar ta hana safarar haramtattun kuɗi ta Najeriya ta 2011 wadda sashen na 15 (3) ya fitar da hukuncin ga mai laifi.

Hukumar EFCC ta kuma ce laifukan sun haɗa da zargin safarar kuɗi miliyan 86 a lokacin da yake darektan kuɗi na ma'aikatar tsaro a tsakanin 2019 zuwa 2021.

EFCC ta ƙara da cewa mai gabatar da ƙara ya samar da shaidu har guda tara a shari'ar da suka hada da wani ma'aikacin bankin Zenith mai suna Eucharia Ezeodi da kuma wani darektan hukumar ma'aikata mai suna Felix Nweke.

Daga nan ne alƙalin ya yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na shekara takwas kan kowane laifin guda 9, inda shekarun suka kama 72. Sai dai kuma alƙalin ya ce hukuncin zaman gidan kason za su tafi ne a tare.

Wane ne Nwabuoku?

Chukwunyere Nwabuoku ya fara aiki a Cibiyar Nazari Dimokraɗiyya, (CDS).

Daga nan ne kuma ya koma aiki a matsayin babban a tsakanin 1992 zuwa 1995, kafin shekarar 1996 lokacin da aka mayar da shi ofishin akanta janar na Najeriya a matsayin mataimakin babban akanta, har zuwa shekarar 2001.

A 2001 ne kuma ya koma aiki a ofishin shugaban majalisar dattawa har zuwa 2003 a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban majalisar ta dattawa a kan aikin gwamnati.

Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi masa naɗi a ofishin akanta janar a 2019.

Nwabuoku ya riƙe kujerar akanta janar na Najeriya na riƙon ƙwarya bayan dakatar da Ahmed Idris.

Sai dai kuma an cire Nwabuoku daga muƙamin makonni bayan naɗin nasa bisa dogaro da cewa hukumar EFCC na binciken sa.