Taimakon da Faransa za ta iya bai wa Najeriya ta fuskar tsaro

Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan Najeriya da masana tsaro na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da kalaman da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi cewa ya nemi taimakon Faransa a yaƙi da matsalar tsaron ƙasar.

Yayin da yake jawabi lokacin da ƙungiyar gwamnonin ƙasar suka kai masa ziyarar gaisuwar sallah a gidansa da ke birnin Legas, Shugaba Tinubu ya ce ya yi doguwar waya da takwaransa na Faransa game da yadda ƙasar za ta taimaka wa Najeriya magance matsalar tsaron da ke addabarta.

Najeriya na fuskantar ƙaruwar hare-haren ƙungiyoyin ƴanbindiga masu ɗauke da makamai, kama daga masu iƙirarin jihadi zuwa na ƴanfashin daji, da kuma na ramuwar gayya tsakanin manoma da makiyaya.

A baya-bayan nan ma an samu tashin bama-bamai a birnin Maiduguri da ƙaruwar hare-haren ISWAP kan sansanonin soji a jihar ta Borno.

Tuni dai Amurka ta aike da dakarunta kusan 200 da jirage marasa matuƙa domin taimaka wa dakarun Najeriya kawar da matsalar tsaron da take fuskanta.

Wane taimako Najeriya za ta samu daga Faransa?

Dr Kabiru Adamu shugaban Kamfanin Beacon Security mai nazarin tsaro a yankin Sahel ya ce ɗaya daga cikin ƙudirin da gwamnatin Shugaba Tinubu ta sanya a gaba shi ne samar da wasu makaman da jami'an tsaron ƙasar ke amfani da su a cikin gida nan da 2027.

''Najeriya na da muradin ƙera kashi 40 cikin 100 na makaman da jami'an tsaronta za su riƙa amfani da su a cikin gida'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa kan hakan ne ma gwamnatin ta yi ƙoƙarin sauya dokokin mallakar makamanta.

Dr Kabiru Adamu ya ce kan wannan buƙata gwamnatin Najeriya ke tuntuɓar manyan ƙasashen Turai domin cimma muradinta.

''A baya-bayan nan ta tattauna da ƙasashe irinsu Birtaniya da Faransa da niyyar su taimaka wa Najeriya, wadda dai ta fi tasiri ita ce wadda ta ƙulla da Turkiyya, wadda ke nuna irin alaƙar da ke tsakanin Najeriya da wasu manyan ƙasashen Turai.

Mece ce alaƙar Faransa da Najeriya ta fuskar tsaro?

Masanin tsaron ya ce da jimawa akwai alamun da ke nuna cewa gwamnatin Tinubu na da alaƙa mai karfi da ƙasar Faransa.

''Kuma an ga lokuta da dama da dakarun faransa ke shiga Najeriya bisa hulɗar dimpomasiyyar soji'', in ji shi.

Ya ce Najeriya na da wakili a ɓangaren soji a ƙasar Faransa haka ita ma Faransa tana da wakili a Najeriya a ɓangaren soji.

''Kuma ƙarƙashin wannan akwai bututuwa da ake yi na taimaka wa juna, kamar horon soji da sauran abubuwan da suka shafi tsaro'', in ji shi.

Faransa za ta iya kawo ƙarshen matsalar tsaron Najeriya?

Dangane da ko Faransa za ta iya kawo ƙarshen matsalar matsalar tsaron Najeriya, shugaban kamfanin Beacon Security ya ce baya tunanin hakan zai iya faruwa.

Sai dai ya ce Waɗannan yarjejeniyoyi da neman taimakon ƙasashen duniya, ɗaya ne daga cikin dabarun tsaro uku da gwamnatin Tinubu ke amfani da su da suka haɗa da alaƙa tsakanin ƙasashe da sauran abubuwa na cikin gida.

To sai dai Dr Kabiru Adamu ya yi gargaɗi game da ƙulla hulda da ƙasashen Yamma musamman Amurka ta Faransa.

''Amurka da Faransa ne manyan ƙasashen da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a Najeriya suka fi tsana, don haka sai gwamnati ta yi taka tsan-tsan wajen neman taimakon taimakon ƙasashen'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa idan Najeriya ta karkata neman taimakon waɗannan ƙasashen biyu, to babu shakka, waɗanan ƙungiyoyi za su sanya wa Najeriya ido.

''Kuma a baya-bayan nan mun ga yadda suka zafafa hare-hare, don haka yana da kyau gwamnati ta sanya lura sosai'', in ji shi.

Tinubu ya raina taimakon Amurka ne ko ƙari ake so?

Shugaban kamfanin na Beacon Security ya ce tsarin da gwamnatin Tinubu ke amfani da shi, bai dogara da ƙasa ɗaya ba dangane da ƙulla yarjejeniyar tsaro.

"Babban abin da ta sanya a gaba shi ne hulɗa da ƙasashe da dama domin cimma muradinta, na magance matsalar tsaro'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa a ƙarƙashin wannan yarjejeniya gwamnatin ke hulɗa da Amurka da Birtaniya da Turkiyya da Faransa da ma sauran ƙasashe.

Sai kuma masanin tsaron ya ce hulɗar Najeriya da kudancin duniya ta fi taimaka mata.

''Domin idan ka duba Turkiyya wadda tuni tana nan tana taimaka wa Najeriya wajen ƙirƙirar jirage marasa matuƙa, saɓanin su sauran ƙasashen waɗanda burinsu shi ne sayar mata nasu, maimakon taimaka mata ta ƙirƙiri nata'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Mene ne tasirin taimakon ƙasashe da yawa?

Dr Kabiru Adamu ya ce ɓangarorin tsaro da ake da su a Najeriya sun kai 42 zuwa 43, kuma kowanne na da matuƙar muhimmanci, don haka yana da kyau a inganta su duka.

''Rundunonin sojin Najeriya ɗaya ne daga cikin waɗannan rundunoni'', in ji shi.

Haka ma akwai cibiyoyin nazarin tsaro da tsare-tsare da dokokin gudanar da tsaro.

''Abu na gaba shi ne irin wannan alaƙa tsakanin Najeriya da wasu ƙasashe, don haka babu yadda za a yi a tsaya a kan guda ɗaya a ce ita ce za ta magance matsalar'', in ji shi.

Ya ce yana da kyau gwamnatin Najeriya ta inganta sauran fannonin tsaron da take da su a cikin gida maimakon hangen na waje.

''Yanzu ka ga ita kanta majalisar tsaro ta ƙasa ta jima ba ta yi zama ba'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa akwai dai da dama da za a inganta a cikin gida, domin ƙarfafa tsaron.