Ina Salah zai koma idan ya bar Liverpool?

Lokacin karatu: Minti 4

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Masar, Mohamed Salah ya ce zai bar Liverpool a ƙarshen wannan kaka. To amma tambayar da masoya da masu bibiyar ƙwallon ƙafa ita ce ina zai koma da taka leda?

Salah, ya sanar da cewa zai bar Liverpool, bayan ya shafe shekaru tara a ƙungiyar tun bayan da ya koma kulob ɗin daga AS Roma a shekarar 2017.

Salah, mai shekaru 33, ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, inda ya ce lokaci ya yi da zai yi bankwana da kulob É—in da ya bayyana a matsayin "gida".

"Kun ba ni mafi kyawun lokaci a rayuwata. Wannan kulob ɗin zai ci gaba da zama gida a gare ni. Barin kulob ba abu ne mai sauƙi ba," in ji shi.

Ita ma Liverpool ta tabbatar da cewa Salah zai bar ƙungiyar idan kwantiraginsa ya ƙare.

Salah shi ne É—anwasan da ya fi samun kyaututtuka a tarihin gasar Fimiyar Ingila.

A tsawon shekarun da ya shafe a Anfield, Salah ya ci kwallaye 255 a wasanni 435, inda ya taimaka wa ƙungiyar lashe kofuna da dama ciki har da gasar Firimiya biyu da kofin Zakarun Nahiyar Turai.

Masana harkokin wasanni Alex Crook, Ben Jacobs da Fabrizio Romano duk sun ruwaito cewa kulob din ya amince Salah ya tafi ba tare da wani sharaÉ—i ba, duk da cewa a baya kwantiraginsa zai kai har shekarar 2027.

Dama an daÉ—e ana raÉ—e-raÉ—in cewa Salah zai ba Liverpool.

Yayin da ɗanwasan mai shekaru 33 ya fara shirin bankwana da ƙungiyar, ga wasu wurare da ake hasashen Salah zai koma taka leda.

Saudiyya

An daɗe ana alaƙanta Salah da komawa buga wasa a Saudiyya.

An fara jita-jitar komawarsa ƙungiyoyin Saudiyya ne tun a shekarar 2025 da kwantiraginsa ke shirin ƙarewa, amma kuma sai ya sake sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Anfield.

Su ma ƙungiyoyin Saudiyya sun daɗe suna neman ɗanwasan, amma ba su samu damar hakan ba. Yanzu da aka tabbatar Salah zai ba Liverpool, ƙungiyoyin Saudiyya za su iya sake yunƙurin neman sa.

A farkon watan Disambar shekarar 2025, rahotanni sun ce ƙungiyoyin Saudiyya sun taya ɗanwasan a kan kuɗi Fam miliyan 100.

Akwai yiwuwar su sake dawowa yanzu da sabon tayin da ba lallai ya kai haka ba.

MLS (Amurka)

Wani wurin da ake hasashen Salah zai iya komawa shi ne buga gasar MLS a Amurka.

BBC ta samu bayanan cewa akwai yiwuwar Salah "zai koma" buga gasar MLS a wannan kaka.

Ana kuma ganin idan ɗanwasan ya tafi Amurka zai fi samun tyi mai gwaɓi.

ƴanwasan da suke kan ganiyarsu na son komawa Amurka saboda ƙungiyoyin gasar MLS ba su tayin banza, inda suke zuɓa maƙudan kuɗaɗe domin samun wanda suke so.

Ko a wannan satin, Antoine Griezmann, ya koma taka leda a Orlando City.

Shahararrun Æ´anwasa irinsu Lionel Messi da Luis Suarez ma suna buga wasa a Inter Miami. Thomas Muller yana Vancouver Whitecaps ga kuma Heung-Min Son da ya koma LAFC a shekarar da ta gabata.

Galatasaray

Ana ganin ƙungiyar Galatasaray ma za ta iya yunƙurin neman Salah, saboda tana da ƙoƙarin jan fitattun ƴanwasa zuwa Istanbul, kamar yadda TNT sport ta ruwaito.

Yawancin ƴawasan da ke gargarar ritaya a fagen taka leda sun yawan tafiya kulob din, inda suke da damar samun tayi mai gwaɓi da kuma buga gasar Zakarun Turai.

Misalai na baya-bayan nan su ne Æ´anwasan gaba da kulob É—in ta ja zuwa Victor Osimhen, Mauro Icardi, Leroy Sane and Didier Drogba su ne Victor Osimhen, Mauro Icardi, Leroy Sane da Didier Drogba

Akwai yiwuwar Salah ya ta fi can domin ci gaba da haska tauraruwarsa.

A Disambar shekarar da ta gabata ma, an ruwaito cewa Galatasaray na shirin ƙulla yarjejeniya da Salah a yayin cinikayyar ƴanwasa a watan Junairu.

Barcelona

Ana hasashen ɗanwasan na ya taɓa yunƙuri komawa Barcelona daga Liverpool.

An ruwaito cewa, a shekarar 2024 Barcelona tana cikin masu neman Salah, kafin daga bisani bisani ta ci gaba da riƙe shi.

Barcelona dama tana yawan É—aukar tosffin Æ´anwasan gaba. Alal misali, Robert Lewandowski.

Sai dai ana ganin yayin da tauraruwar matasan Æ´anwasa irinsu Pedri, Lamine Yamal, Alejandro Balde, Fermin Lopez da Pau Cubarsi ke haskawa, ba lallai Salah ya taka rawar gani idan ya je Barcelona.