Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na nazari kan Lewis-Skelly, Silva na son tafiya Barcelona
Manchester United na duba yuwuwar neman matashin dan bayan Arsenal na gefen hagu, Myles Lewis-Skelly na tawagar Ingila, mai 19. (Teamtalk)
Shi kuwa dan wasan tsakiya na Manchester City Bernardo Silva, mai shekara 31, ya fi son tafiya Barcelona idan kwantiraginsa da City ya kare a karshen kakar nan, sai dai yana fargabar cewa akwai isassun matasan 'yan wasan tsakiya a kungiyar ta Sifaniya. (Sport)
Dan wasan tsakiya na Newcastle United Bruno Guimaraes, mai shekar 28, na kan gaba a jerin wadanda Manchester United ke son zawarci domin maye gurbin Casemiro, mai shekara 34, kuma tuni har kungiyar ta tattauna da wakilan dan Brazil din. (UOL)
Haka kuma Manchester United din na ganin za ta fuskanci gogayya a kan, dan wasan tsakiya na Chelsea Andrey Santos mai shekara 21, inda West Ham da Juventus ma ke son dan Brazil din. (CaughtOffside)
Ita ma Inter Milan na sa ido a kan Santos din kuma za ta iya zawarcinsa a bazara. (Calciomercato)
Hankalin Robert Lewandowski, mai shekara 37, ya rabu kan ko ya kara shekara daya a Barcelona ko kuma ya tafi wata kungiyar a Amurka. (Fabrizio Romano)
Tottenham wadda ke cikin halin kaka-ni-ka-yi na nazari kan makomar kociyanta na rikon-kwarya Igor Tudor. (Telegraph)
AC Milan ta nuna sha'awarta kan sayen dan wasan tsakiya na Bayern Munich Leon Goretzka, idan wa'adin zaman dan wasan na Jamus mai shekara 31 ya kare a bazara. (Christian Falk)