Man United na zawarcin Ndidi, Rashford zai ci gaba da zaman aro a Barca

Lokacin karatu: Minti 2

Kungiyar Barcelona na son ci gaba da rike dan wasan gaba na Manchester United, Marcus Rashford mai shekaru 28, a matsayin aro na wata kakar wasan domin kauce wa biyan fam miliyan 26 da ake neman don sayar masu da shi (Daily Mail).

Manchester United na iya kokarin daukar dan wasan tsakiya na Najeriya Wilfred Ndidi mai shekaru 29 daga Besiktas, yayin da mai tsaron ragar Turkiyya Altay Bayindir mai shekaru 27 zai iya komawa can (SporX).

Kungiyar Borussia Dortmund na ganin za ta iya shawo kan dan wasan Manchester United Jadon Sancho mai shekaru 25 ya koma kungiyar a karo na uku (The Times).

Manchester United na da sha'awa kan dan wasan tsakiya na Italiya Sandro Tonali, amma Newcastle United za ta nemi sama da fam miliyan 100 kan dan wasan mai shekaru 25 (The i).

Kungiyar Juventus na iya sayen dan wasan gaba na Netherlands Joshua Zirkzee daga Manchester United kan kusan euro miliyan 25 (fam miliyan 21.6), ko kuma ta dauke shi aro tare da zabin saya daga baya (Tuttosport).

Dan wasan tsakiya na Senegal Lamine Camara na cikin jerin 'yan wasan da Newcastle ke nema, kuma zai iya barin Monaco a wannan bazara (Football Insider).

Newcastle na sha'awar daukar mai tsaron raga na Faransa Robin Risser mai shekaru 21 daga Lens (Sky Sports Switzerland).

Kungiyar West Ham United na shirin tattaunawa da Chelsea domin mayar da aron dan wasan bayan Faransa Axel Disasi mai shekaru 28 ya zama na dindindin (Football Insider).

Chelsea da Tottenham Hotspur na zawarcin dan wasan gaba na Hoffenheim, Fisnik Asllani mai shekaru 23 (Bild).