Man Utd za ta rike Mainoo da Maguire, Liverpool ba za ta samu Bastoni ba

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan tsakiya na Manchester United Kobbie Mainoo, mai shekara 20, zai tsawaita zamansa a kungiyar har zuwa 2031, inda za a kara masa albashi ninki hudu - ya rika karbar fam120,000 a duk mako. Haka shi ma Harry Maguire, ana sa ran Old Trafford din za ta tsawaita zamansa. (Talksport).
Newcastle na son sayen dan wasan Chelsea mai kai hari Liam Delap, dan Ingila, mai shekara 23 a bazara a kan kudin da ya kai fam miliyan 40. (Talksport).
Fatan Liverpool na shawo kan Inter Milan ta sayar mata da dan bayanta na tawagar Italiya Alessandro Bastoni, mai shekara 26, na zagwanyewa. (Teamtalk).
Tottenham na sa ido a kan mai tsaron ragar Jamus Noah Atubolu, mai shekara 23, yayin da golan kungiyar ta Firimiya na yanzu Guglielmo Vicario ke shirin komawa Inter Milan. (Mail).
Everton ta ce ba za ta sayar da dan wasanta na tsakiya Kiernan Dewsbury-Hall, mai shekara 27, dan Ingila ba ko nawa za a ba ta duk da sonshi da Manchester United ke yi. (Teamtalk).
Kociyan Newcastle United Eddie Howe ya bayyana rahoton da ke cewa dan wasansu na tsakiya Bruno Guimaraes, dan Brazil zai iya tafiya Manchester United a matsayin cin-fuska ga kungiyar ta Magpies, da kuma shi kansa kyaftin din nasu mai shekara 28. (Sky Sports).
Manchester United da Liverpool na daga cikin kungiyoyin da ke son dan bayan Fulham Antonee Robinson, mai shekara 28, wanda ke buga wa tawagar Amurka wasa. (Caught Offside).
Kociyan Bournemouth Andoni Iraola na daya daga cikin na gaba-gaba da za a zaba domin maye gurbin kociyan Athletic Bilbao bayan da Ernesto Valverde ya yanke shawarar ajiye aiki. (Marca).
Tottenham da Crystal Palace ma na son Iraola, kasancewar dukkaninsu suna neman kociya da za su dauka a bazara. (Mail).














