Wasu manyan ƙungiyoyi na fafatawa kan Bruno Guimarae, Guardiola zai bar Man City

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na tattaunawa domin sayen kyaftin ɗin Newcastle United, wato Bruno Guimaraes, kan kusan fam miliyan 69. Sai dai Real Madrid ke nunawa na iya dagula yarjejeniyar. (Reuters)
Manchester United za ta ƙi yarda da yunƙurin Barcelona na tsawaita aron Marcus Rashford, inda suka ce ko dai a biya fam miliyan 26 da aka amince ko kuma a dawo da shi Old Trafford. (Mirror)
Mai tsaron baya na Tottenham Hotspur, Cristian Romero, ya yi watsi da rade-radin komawa wata ƙungiya, yana mai cewa ya maida hankali ne kan taimaka wa kulob ɗin gujewa nutsewa daga gasar Premier. (Independent)
A gefe guda, ɗan wasan gaba Randal Kolo Muani, wanda ke zaman aro a Tottenham Hotspur daga Paris Saint-Germain, na shirin komwa Juventus dindindin. (Gazzetta dello Sport)
Ɗan wasan gaba na Liverpool, Mohamed Salah, bai yanke hukunci kan makomarsa ba duk da sha'awar da ake nunawa kansa a Saudiyya, yayin da Al-Hilal ke son jawo daraktan wasanni Richard Hughes. (Mail)
Real Madrid na tattaunawa da Antonio Rudiger kan sabon kwantiragi. (Marca)
Borussia Dortmund na sha'awar sake ɗaukar Jadon Sancho, wanda ke aro a Aston Villa, yayin da kwantiraginsa da Manchester United zai ƙare a watan Yuni. (Athletic)
Manchester City na ƙara ganin yiwuwar barin koci Pep Guardiola a ƙarshen kakar wasa, kuma ana duba masu maye gurbinsa. (Football Insider)
Mai tsaron raga na Tottenham Hotspur, Guglielmo Vicario, na cikin waɗanda Inter Milan ke nema, kuma yana iya amincewa da komawa Serie A. (Calciomercato)
Mai tsaron raga na Brighton & Hove Albion, Carl Rushworth, wanda ke zaman aro a Coventry City, ya ja hankalin kusan kulob shida na Premier League, kuma ana sa ran zai kai kusan fam miliyan 20. (Talksport)












