Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zidane zai karbi Faransa, Manchester United na son Guimaraes
Tsohon kociyan Real Madrid Zinedine Zidane ya amince ya karbi aikin horad da tawagar Faransa, bayan gasar cin Kofin Duniya. Zidane mai shekara 53 wanda ya ci kwallo sau biyu a wasan karshe da Faransa ta ci Kofin Duniya na gasar 1998, zai maye gurbin Didier Deschamps, mai shekara 57. (ESPN)
Dan wasan gaba na gefe na Manchester United Jadon Sancho, wanda yanzu yake zaman aro a Aston Villa, ya tattauna da Borussia Dortmund a kan komawarsa kungiyar ta Jamus, a matsayin wanda ba wani kwantiragi a kansa. Haka kuma dan wasan na Ingila mai shekara 25 ya yarda a rage yawan albashinsa. (Sky Sports Deutschland)
Manchester United na sha'awar sayen dan wasan baya na gefe na bangaren hagu Alphonso Davies daga Bayern Munich, a bazaran nan, kuma daman kungiyar ta Jamus a shirye take ta karbi tayi a kan dan wasan na tawagar Kanada, mai shekara 25l. (CFBayerninsider)
Haka kuma Manchester United din na son kyaftin din Newcastle Bruno Guimaraes, inda rahotannin daga kasar dan wasan mai shekara 28, Brazil ke nuna alamun cewa kila a sayar da shi a kan fam miliyan 60.(Sports Illustrated)
A shirye tsohon kociyan Brighton da Marseille Roberto de Zerbi, yake domin zama sabon kociya na dindindin na Tottenham, amma idan kungiyar ta ci gaba da zama a gasar Firimiya. (Telegraph)
Har yanzu Manchester United ba ta tuntubi kowa ba cikin wadanda za ta zaba ya zama sabon kociyanta na dindindin a bazara, kuma shugabannin kungiyar ba za su yi gaggawa ba a kan lamarin. (Sky Sports)
Har yanzu manyan shugabannin Newcastle suna da kwarin gwiwa a kan kociyan kungiyar Eddie Howe, wanda ke cikin matsin lamba. Ana sa ran yin gagarumin garambawul na 'yan wasa a kungiyar a bazara, inda za a sayo sababbi a kuma sayar da wasu. (Mail)
Ana kallon matashin dan bayan Chelsea Josh Acheampong, dan Ingila mai shekara 19, a matsayin wanda zai dace da Crystal Palace, yayin da alamu ke nuna cewa kila ya bar Stamford Bridge a bazaran nan. (Football Insider)
Kungiyoyin Jamus - Schalke da Hannover, na son dan wasan tsakiya na Leeds da Japan Ao Tanaka, mai shekara 27. (Teamtalk)
Dan wasan gaba na Faransa Antoine Griezmann, mai shekara 35, zai kawo karshen zamansa na kaka goma a Atletico Madrid a bazara, inda zai tafi kungiyar Orlando City ta gasar Amurka. (Times)