Wane ne Bako Gorgore, kwamandan ISWAP da ya jagorancin kisan Shekau?

..

Asalin hoton, Zagazola/x

Lokacin karatu: Minti 4

Rahotonni daga Najeriya na cewa dakarun sojin ƙasar sun kashe ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar ISWAP, mai suna Malam Bako Gorgore, da aka fi sani da Abou Mustapha.

Bayanai sun nuna cewa Bako Gorgore ya gamu da ajalinsa ne a wata arangama da jami'an tsaro a yankin Tafkin Chadi.

Ɗaya daga cikin fitattun masu bincike kan ayyukan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a Najeriya, Zagazola makama na daga cikin waɗanda suka yi iƙirarin kisan Malam Bako.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, fitaccen mai bincike kan ƙungiyoyin ƴanbindigar a Najeriya ya ce dakarun rundunar Hadin Kai ne suka kashe Gorgore a wata arangama a yankin ƙaramar hukumar Kukawa na jihar Borno.

Ya ce an tabbatar da labarin ne ta hanyoyin tattara bayanan sirri masu yawa.

Dr Kabiru Adamu shugaban Kamfanin Beacon Security mai nazarin tsaro a yankin Sashel ya ce bayanan da suka samu sun tabbatar musu da kisan Bako Gorgore.

''Hanyoyi da dama da muke tattara bayanan sirri da tantance su, sun tabbatar mana da labarin kashe shi,'' in ji Kabiru Adamu.

Zagazola ya yi ikirarin cewa majiyar soji ta tabbatar masa cewa jami'an tsaron sun yi kutse a wayoyin jagororin ISWAP ɗin, inda suka tabbatar da mutuwar Mallam Bako.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga rundunar sojin ƙasar da ta tabbatar da kisan duk da cewa labarin nasara ce a gare ta wani abu da ta saba gaggauta fitarwa da zarar hakan ta faru saɓanin rashin nasara.

A baya-bayan nan mayaƙan ISWAP sun tsananta hare-hare musamman kan sansanonin soji a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wane ne Bako Gorgore?

Mallam Bako

Asalin hoton, Zagazola Makama

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Zagazola Makama ya ce Malam Baƙo, da aka fi sani da Abou Mustaph a ƙungiyar ISWAP, ɗan asalin ƙaramar hukumar Yunusari ne a jihar Yobe da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Mutum ne da ya manyanta, wanda ake tunanin shekarunsa sun kai kimanin 60, a cewar Makama.

Ya kasance cikin na farko-farkon gwagwarmayar Boko Haram, tun lokacin kafuwarta a shekaraun 2000, ƙarƙashin jagorancin Shugabanta na farko, Muhammad Yusuf.

Cikin wata hira da BBC a kwanakin baya, Dr. Audu Bulama Bukarti, ɗaya daga cikin manyan masu bincike kan ƙungiyoyin yanbindiga a ƙasashen Afirka ya bayyana Malam Bako Gorgore a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin ISWAP.

Bayanai sun nuna cewa Mallam Bako ya shafe shekaru yana jagorantar ayyukan ƙungiyar ISWAP ta hanyar riƙe muƙamai daban-daban a yankin Timbuktu, wani yanki mai daji da tsaunuka a arewacin Borno kusa da Tafkin Chadi.

''Tsakanin 2018 zuwa 2021, ya riƙe muƙamin babban kwamandan ƙungiyar mai kula da yankin Furuuk na Timbuktu, bayan ƙarewar wa'adin kwamandan da ke kula da yankin, mai suna Mustapha Krimima'', a cewar Zagazola Makama.

Ya ci gaba da cewa bayanan sirri sun nuna cewa a wannan lokaci an bayyana Malam Bako a matsayin ɗaya daga cikin masu shirya ayyukan ƙungiyar, ciki har da hare-hare da kula da motsin mayaƙa da safarar makamansu a yankin Tafkin Chadi.

Dr Kabiru Adamu ya tsakanin 2021 zuwa 2022, an yi hasashen cewa Bako zai iya zama shugaban ƙungiyar ISWAP bayan kashe manyan jagororin ƙungiyar a wancan lokaci.

Rawar da ya taka a kisan Shekau

Ɗaya daga cikin manyan lokutan da suka ƙara fito da Gorgore shi ne rikicin da ya ɓarke a ƙungiyar Boko Haram da ISWAP a 2021.

Rikicin da ya yi sanadin mutuwar shugaban Boko Haram na wancan lokaci wato Abubakar Shekau.

''Majiyoyin tsaro sun ce Bako Gorgore na daga cikin manyan kwamandojin ISWAP da suka jagorancin mayaƙan ISWAP zuwa dajin Sambisa, domin gwabzawa da ɓangaren Shekaru a 2021'', a cewar Zagazola Makama.

Rahotonni a lokacin sun ce Shekau ya tayar da abin fashewa domin halaka kansa a lokacin gumurzun, maimakon ya miƙa wuya da ɓangaren ISWAP.

Lamarin da ya karya logon ƙungiyar Boko Haram tare da ƙarfafa ɓangaren ISWAP, a cewar masana tsaro.

Yadda ya samu babban matsayi a ISWAP

Zagazola Makama ya ce bayan sake fasalin tsarin shugabanncin ISWAP, Gorgore ya ci gaba da nuna tasirinsa a ƙungiyar.

''A 2022 aka ɗaga matsayinsa, inda ya samu shiga mamba a majalisar shura ta ƙungiyar, mataki mafi girma na ɗaukar matakai a ƙungiyar, wanda ya yi daidai da tsarin shugabancin ƙungiyar IS a faɗin duniya'', a cewar Makama.

Kafin ɗaga darajarsa zuwa majalisar shura, Bako Gorgore ya taɓa riƙe muƙamin Amir Jaysh, na kungiyar, wato shugaban dakarun mayaƙan ƙungiyar a yankin Timbuktu.

''Aikinsa a wannan lokaci ya ƙunshi, lura da mayaƙan ƙungiyar, da shirya kai hare-hare da kula da al'amuran ƙungiyar a yankin Tafkin Chadi'', in ji shi.

Iƙirarin mutuwarsa a baya

A 2022 an taɓa yaɗa iƙirarin cewa ya mutu a wani hari ta sama da sojojin Najeriya suka kai wa mayaƙan ISWAP a yankin Tafkin Chadi.

Sai dai daga baya ta tabbata bai mutu ba, inda bayanan sirri suka tabbatar da cewa raunuka ya samu a harin, a cewar Makama.

Idan har ta tabbata ya mutu ana ganin kisan nasa babbar nasara ce a yaƙi da ƙungiyar ISWAP da sojojin Najeriya ke yi.

''Ba ƙaramar nasara ba ce a matsayinsa na babban jagora cikin kwamitin Shura, wanda kuma ya samu gogewa tun a ƙungiyar Boko Haram, ba shakka kisansa zai wargaza tsarin shugabancin ƙungiyar'', in ji Makama