Me ya sa hare-haren Boko Haram suka ƙazanta a watan Ramadan?

Asalin hoton, Reuters
A daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Sallah a Najeriya da ƙasashen duniya, mutanen jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya fargaba suke ta komawar hare-haren Boko Haram.
A ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu ne dai maharan da ake kyautata zaton ƴan Boko Haram suka tayar a bama-bamai a gab da asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri da babbar kasuwar Litinin da ake kira 'Monday Market' da kuma ofishin aikewa da saƙonni ko gidan waya.
Hare-haren sun auku ne jim kaɗan bayan mayaƙan na Boko Haram sun kai wasu hare-haren a sansanonin sojin Najeriya da ke Ajari da Baga da kuma Damboa duk a jihar ta Borno.
Wani da lamarin ya faru a kusa da wajen da suka yi buɗa-baki ya shaida wa BBC cewa ''Mun sha ruwa muna zaune, sai kawai jin ƙara muka yi, sai kuma ga mutane suna gudu wasu cikin jini, to muma dai daga nan sai kowa ya kama gaban shi. Da idona dai na ga mutanen da suka jikkata babu adadi.''
Har yanzu dai babu tabbacin adadin waɗanda suka rasu a hare-haren na Boko Haram ba, duk da cewa hukumomin ƙasar sun tabbatar tare da aik jaje kan aukuwar lamarin.
Wannan na zuwa ne a daidai lokaci da ake cigaba da tattauna batun hare-haren da mayaƙa suka kai wa a sansanin sojin Najeriya, lamarin da wasu ke ganin kamata ya yi sojojin su riƙa farautarsu a maɓoyarsu.
A kwanakin baya ne a cikin mako ɗaya tal, rundunar sojin Najeriya ta rasa kwamandojin sojin ƙasar guda uku a hare-haren da Iswap ta kai a wurare daban-daban a lokutua daban-daban.
Me ya sa a watan Ramadan?
Shugaban Najeriya ya umarci manyan hafsoshin tsaron ƙasar su gaggauta komawa birnin Maiduguri na jihar Borno, inda aka kashe aƙalla mutum ashirin da uku a harin bama-bamai a jiya Litinin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani abu da ke jan hankalin mutane game da waɗannan sababbin hare-haren su ne yadda suke aukuwa a watan Ramadan, da kuma yadda suke yi kan masu ko dai ibadar azumi ko masu sallah.
Wata majiyar tsaro da ba ta so a ambaci sunanta ta ce sun samu rahoton cewa mayaƙan sun ce za su zafafa kai hare-haren ne a goman ƙarshe saboda a daidai lokacin ne aka yi yaƙin Badar a zamanin Annabi Muhammad.
Majiyar ta ƙara da cewa wannan ne ya sa sojojin da sauran jami'an tsaro suka fara aikin kar-ta-kwana domin daƙile yunƙuri ko barazanar.
A cikin wannan watan na Ramadan dai sassan Najeriya sun fuskanci hare-hare masu zafi, daga na Boko Haram zuwa na ƴanbindiga da sauransu.
Malam Kabiru Adamu mai bincike a harkokin tsaro a yankin Sahel, kuma shugaban kamfanin Beacon security and consulting, ya ce akwai bayanai da ke nuna cewa asaliln uwar ƙungiyar ce ta buƙaci haka.
"Mun samu bayanan da ke cewa babbar ƙungiyar ce ta buƙaci su ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare."
Masanin tsaron ya ce asalin burin mayaƙan shi ne kafa daular Musulunci, "amma a fahimtarsu duk wanda ba ya bin aƙidarsu, ba Musulmi ba ne. Duk da yake akwai bambancin Boko Haram da Iswap. Amma haƙƙin gwamnati ne ƙoƙarin tabbatar da cewa mutane sun fahimci abin da ke faruwa kuma tabbatar sun yi tir."
Hare-hare a ƙwaryar Maiduguri

Rikicin Boko Haram ya fara ne tsakankanin shekarar 2009, inda Maiduguri ya zama birnin da lamarin ya fi ƙamari.
Sai dai an ɗan sauƙin hare-hare a ƙwaryar birnin na tsawon lokaci, inda ya kasance ƙauyuka da garuruwa bayan gari ne ke cigaba da fama.
A game da abin da masana suke gani kan yawaitar sababbin hare-haren ga tsaron ƙasa, Kabiru Adamu ya ce akwai alamu da ke nua cewa mayaƙan na Boko Haram suna so ne koma cikin Maidduguri.
"Wanda ya ke bibiyar hare-haren na baya-bayan nan zai fahimci cewa niyyarsu ita ce ta shiga ƙwaryar Maiduguri, wannan babban nakasu ne ga tsaron Najeriya," in ji masanin na tsaro.
Ya ƙara da cewa aikin gwamnati na magance matsalar tsaro, domin a cewarsa, maharan sun ce za su yi, kuma sun samu nasara, "abin jira shi ne ko za su iya cigaba da haka."
Masanin tsaron ya ƙara da cewa mayar da hannu baya ya nuna akwai saurin aiki a jami'an taro da ma gwamnati.
"Sun ɗauki wannan dabarar ce domin nuna cewa ba a ci galaba ba a kansu, domin su nuna cewa sun da sauran ƙarfinsu."
'Yadda muka tsira'
Hukumomi sun ce bincike farko-farko ya nuna cewa mahara masu ƙunar baƙin-wake ne suka kai hare-hare, sannan rundunar ƴansandan jihar sun tabbatar da harin, tare da cewa tuni sun fara bincike.
Wani mazaunin garin mai suna Modu Bukar, wanda ganau ne a harin kasuwar Litinnin, ya bayyana wa AFP cewa suna zaune ne kawai suka ji ƙarar fahewa, "shi ne sai aka fara guje-guje."
Shi ma Mala Mohammed mai shekara 31 ya faɗa wa AFP cewa, "da muka ji ƙara sai mutane suka fara gudu zuwa ofishin aika saƙo saboda babu nisa da ƙofar shiga kasuwar."
Ya ce mutane suna cikin gudun ne, "sai wani maharin ya kutsa cikinsu shi ma," in ji shi.
Kafin hare-haren, jami'an tsaro sun daƙile yunƙurin kai wani harin a sansanin soji da ke Ajilari.










