Shin Iran za ta iya galaba kan Amurka?

Iran

Asalin hoton, Reuters/Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

A daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi kan Iran, har yanzu babu alƙaluma da za su tabbatar da ɓangaren da ke samun nasara a zahiri.

Shugaban Amurka Donal Trump dai ya sha nanata cewa ya riga ya gama da Iran, musammam yadda yake yawan ambaton cewa ya tarwatsa rundunar sojin ƙasar ta ruwa da sama da sauransu.

Sai dai ganin yadda Iran ke ƙara nuna ƙwanji, da cigaba da kai hare-hare musamman a sansanonin sojin Amurka a ƙasashen Gabas ta Tsakiya, sai ake ganin tamkar akwai sauran rina a kaba.

Haka kuma Mista Trump ya bayyana cewa komai na Iran ya ƙare, sannan ɗan sauran da ya rage ɗin ma yana ɗaga ƙafa ne, inda ya yi iƙirarin cewa Iran ɗin ma ta fara neman a shiga yarjejeniyar tsagaita wuta.

Sai dai hukumomin Iran sun musanta batun neman a tsagaita wuta, inda suka bayyana cewa a shirye suke su ci gaba da gwabza yaƙi har sai baba ta gani.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce "an lalata tsaron sararin samaniyarsu, da ƙarfin sojin ruwansu, da tsarin shugabancinsu."

Ya ƙara da cewa: "Suna son a tattauna. Amma na ce musu lokaci ya ƙure!"

A martanin da ta mayar, Iran ta ce tana kare kanta ne ta hanyar ƙaddamar da hare-hare kan Isra'ila da wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya da Amurka take da sansanonin soji a ciki.

Domin sanin haƙiƙanin irin nasarorin da kowane ɓangare yake samu, akwai buƙatar a waiwayi tarihi domin sanin muradun ɓangarorin da manufofinsu na shiga yaƙin tun a farko.

Burin Amurka a yaƙin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Muradun Amurka da shugabanta Donald Trump bai fito ƙarara ba a yaƙin, sai dai an san akwai batun mallakar makamin nukiliya na Iran da batun kifarwa ko sauya gwamnatin Iran.

Sai dai da alamu duk da cewa an kashe jagoran addinin ƙasar, tuni wani ya maye gurbinsa, kuma kiraye-kirayen da Donald Trump da Benjamin Netanyahu suka yi na Iraniya su fito su ƙwaci gwamnati hakan bai faru ba - masana ma na ganin yaƙi ya ƙara ƙarfafa haɗin kan Iraniyan ne.

Tun kafin fara yaƙin, an fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a birnin Geneva a watan Fabrairu, wadda Oman ta shiga tsakani, inda aka fara samun maslaha.

Oman ta ce Iran ta fara bayyana amincewarta da tsagaita batun mallakar makamin nukiliya, amma dai ba ta amince da daina ƙera makamai masu linzami ba, da ma batun janye jiki daga ƙungiyoyin da ke goyon baya irin su ƴan Houthi a Yemen da Hezbollah a Lebanon.

Amma dai da alama daga cikin manyan muradun Amurka akwai kawar da gwamnatin tsarin mulkin Ayatollah masu ra'ayin riƙau, tare da maye su da masu sassauƙan ra'ayi da suke gani ba ya barazana ga Amurka da maƙwabtata.

Wani abu da Amurka za ta so shi ne ta gajiyar da Iran, har ta bayar da kai bori ya hau. Amma shi ma wannan da wahalar gaske, ganin har yanzu ƙasar na ƙara nuna ƙwanji ne.

Sannan datse mashigar Hormuz da Iran ta yi ya ƙara jefa duniya cikin matsalar makamashi, lamarin da ke ƙara nuna cewa Amurka za ta yi duk mai yiwuwa wajen buɗe mashigar to amma kuma sai ga shi tana neman tallafin sauran ƙasashen duniya.

Mohammad Qaddam Siddiq Isa wani mai sharhi ne a kan al'amuran da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya ya ce, Amurka za ta so ta hana Iran mallakar makamin nukiliya.

Sai dai ya ce Amurka ba ta matsa sai ta kifar da gwamnatin Iran ba, inda ya ce idan ta samu jagoranci samar da canji ma kaɗai, za ta ce ta samu nasara.

Me Isra'ila ke so?

A nata ɓangaren, Isra'ila tana da burin ganin an ƙarar da makaman Iran masu linzami ko kuma a tarwatsa su, sannan a tarwatsa sansanonin sojin ƙasar.

Sai dai duk cibiyoyi za a iya sake gina su ko da an ruguza, amma Isra'ila na so ta ƙara nuna wa Iran cewa a shirye take ta ƙara ruguza su ko da an sake ginawa a cikin watanni kaɗan.

Isra'ila dai na ganin makaman Iran masu linzami da ma zargin ta da yunƙurin mallakar makamin nukiliya a matsayin babbar barazana.

Iran na da masana'antar ƙefa jirage marasa matuƙa na cikin gida, inda har ta ba Rasha jiragen Shahed marasa matuƙa a yaƙinta da Ukraine.

Haka kuma Iran ta inganta uranium zuwa kashi 60, wanda ya zarce matakin da ake buƙata domin samar da makamashi.

Sai dai Qaddam ya ƙara da cewa ita Isra'ila ta ɗan haura Amurka a buƙatu, inda take da burin ganin an kifar da gwamnatin Iran ɗin baki ɗaya.

Fatan Iran

Iran dai muradunta ba masu yawan ba ne, domin babban burinta shi ne tsallake buƙatun da Amurka da Isra'ila ke da burin samu a yaƙin.

Qaddam ya ce da zarar an kammala yaƙin, amma Amurka da Isra'ila ba su samu nasarar cika buƙatunsu ba, to shi ke nan Iran za ta yi iƙirarin samun nasara a yaƙin da aka gwabza.

Haka kuma Iran na da burin samun tabbacin cewa ba za a kai mata wasu hare-haren ba a nan gaba.

Yanzu yaƙin ya koma kan tattalin arziki, inda rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi ya ja hankalin duniya.

Iran za ta iya samun nasara?

A game da ko Iran za ta iya samun nasara, Qaddam Siddiq ya ce ya danganta da abin da kowane ɓangaren ya lissafa a matsayin nasara.

"Ita dai Iran babbar nasararta ita ce a ƙarƙare yaƙin ba tare da Amurka da Isra'ila sun cimma burinsu ba," in ji shi.

Sai dai a daidai lokacin da Trump ke iƙirarin samun nasara, yana ci gaba da neman taimakon ƙasashen Turai da ƙungiyar da sauransu a yaƙin, musamman ma kan buɗe mashigar Hormuz.

Wannan ya sa wasu suke ganin tamkar akwai farfagadar, lamarin da ya sa zai yi wahalar gaske fahimtar irin nasarorin da ɓangarorin ke samu.

Sai dai wasu ganin yadda Iran ke ci gaba da nuna ƙwanji a yaƙin, da ci gaba da datse mashigar Hormuz da hana kasuwancin makamashi sakat a duniya na nuna cewa ita ma Iran tana rawar hantsi a yaƙin.

Wani abu game da Iran shi ne kasancewar ƙasar ta daɗe da tarihin juriya a yaƙi, sannan tana daga cikin ƙasashen da suka fi yawan rudunar tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

Wani rahoton Cibiyar Nazarin Ƙasa da Ƙasa kan ƙarfin soji a shekarar 2025 ya ce, Iran tana da kusan jami'ai kusan 610,000, cikinsu akwai 350,000 da ke aikin sojin ƙasar da kuma 190,000 da suke rundunar juyin juya hali, waɗanda suke aikin samar da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da kuma wasu ayyuka a yankin.

Haka ma Iran tana dogaro ne kan ƙawancen yankin, ciki har da mayaƙan Houthi a Yemen, da 'yan Hezbollah a Lebanon da mayaƙan ƙungiyoyi a Iraƙi da kuma Hamas.

Nicole Grajewski ya ce duk da wasu takunkumai da Iran ke fuskanta, ƙasar tana da daɗaɗɗen tarihin jurewa dogon faɗa.

Hakan ya samo asali ne tun a yaƙin Iran da Iraƙi, inda aka kai musu hare-hare a birane da dama duk da raunin da take da shi na makaman yaƙi na zamani.