Matakai shida da suka kamata a ɗauka kan tubabbun ƴanbindiga

Asalin hoton, Getty Images
A jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya, tubabbun ƴanbindiga da aka yi sulhu da su a baya sun ƙaddamar da hare-hare tare da kashe mutum 16 a wasu ƙauyuka huɗu na ƙaramar hukumar Jibia bayan wani rikici tsakaninsu da ƴan sa-kai a yankin.
Mazauna garin sun ce tubabbun ƴan bindigar sun kai harin ne bayan samun saɓani da ƴan sa-kan bayan sun yi yunƙurin dakatar da su daga tafiya da wasu shanu da suke zargin na sata ne.
Ko a watan Fabrairun 2020, an gabatar da wani ƙudurin doka gaban majalisar dattawan Najeriya wanda zai bada dama domin sake shigar da tubabbun mayaƙan ƙungiyar Boko Haram cikin al'umma, wanda tsohon gwamnan jihar Yobe Ibrahim Geidam ya gabatar.
Ƙudurin dokar na so a kafa hukumar da za a ɗora wa alhakin ilimantar da kuma sake shigar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al'umma.
Sai dai wasu ƴan Najeriya na nuna damuwa kan yadda suka ce ana bai wa tubabbun ƴanbindiga da Boko Haram muhimmanci, yayin da mutanen da suka raba da muhallansu ke cikin ƙuncin rayuwa a sansanonin ƴan gudun hijira.
Matakan da suka kamata a kansu
Domin jin irin matakan da suka dacewa a ɗauka kan tubabbun ƴanbindiga, Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon security and consulting ya ce akwai sauran aiki a gaban gwamnati.
Ya ce sun daɗe bayar da shawarwari kan abubuwan da suka fi dacewa a yi domin tabbatar da an nasarar aiki, amma a cewarsa ba a yi amfani da su ba yadda ya kamata.
Ya ce matuƙar ana so a samu nasara wajen tabbatar da an tsugunar da tubabbun ƴanbindiga "akwai ƙa'idoji da dama da dole a yi amfani da su. Mafi ƙaranci shi ne a ɗauki wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta tsara."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masanin tsaron ya ce matakan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar su ne:
- Sanin ko su wane ne. Wato a samu cikakken bayanansu.
- Amfani da kimiyya wajen ɗauka da tattara bayansu.
- Sanin na'ukan makamansu kafin karɓe su
- Tsara me za a yi da makaman
- Me za a yi da tubabbun? misali koya musu sana'a ko saka su cikin jami'an tsaro.
- Waɗanda suka yi wa laifi sun yafe ne ko suna buƙatar diyya?
Kabiru Adamu ya ƙara da cewa bincikensu ya nuna cewa ba a yi amfani da ƙa'idojin ba kafin ɗaukar matakin shiga sulhu.
"Kawai an yi gaggawar shiga yarjejeniyar ne, sai kuma aka bar su kara zube. Wannn ba ƙaramin hatsari ba ne ga tsaron ƙasa, kuma ga shi nan an fara gani a jihar Katsina," in ji shi.
Sai dai an daɗe ana nuna yatsa tsakanin gwamnati da ƴanbinigar kan abin da ya sa suke komawa ruwa, lamarin da Kabiru Adamu ya ce babban laifin na gwamnati ne a dukkan matakai.
"Gwamnati ke da laifi, ita ke da haƙƙin tabbatar da doka. A tsarin da muke ciki yanzu akwai abin da ake kira 'social contract' mun hannanta wa gwamnati tsaronmu," in ji shi.
Ya ce ya rage wa gwamnatin ne idan ta ga ta hanyar sulhun ne za ta yi amfani wajen magance matsalar, "to sai ta bi tsari ba tare da wani kamen-kame ba. Ta fito kai tsaye, idan kuma ba sulhun ba ne, to ta bi hanyoyin da suke dace."
Ya ce akwai buƙatar gwamnati ta fito fili ta yi wa gwamnati cikakken bayani kan abin da ake ciki.
"A taƙaice akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta fayace komai kan tsare-tsaren kuma wannan bai hana amfani da ƙarfi ba. Ni ba na tunanin an saɓa sulhu domin an yi amfani da ƙarfi. Dole hukuma ta bayyana ita ce hukuma."
Ya ce idan gwamnati na so ta yi sulhu, zai yi kyau ne ya zama ƴanbindigar ne suka nemi sulhun, ba gwamnati ba.
Yadda za a tabbatar da ɗorewar zaman lafiya
Kabiru Adamu ya bayyana a wata tattaunawarsa da BBC cewa akwai abubuwa masu muhimmanci da gwamnati ya kamata ta yi domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya, musamman a yankunan da ake yawan samun hare-haren ƴanbindiga.
Ga jerin matakan da ya bayar kamar haka;
- Ɗaukar mataki na dindindin wajen magance matsalar tsaro: Kabiru Adamu ya jaddada cewa dole ne gwamnati ta yi amfani da hanyoyi na dindindin wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.
- Amshe makaman 'yan bindiga: Masani ya nuna cewa makaman da ƴn biondigar ke kai mhare-hare da su har yanzu yana hannun su wanda shi ne babban barazana ga zaman lafiya. "Saboda haka, gwamnati ta tabbatar da cewa ta anshe makaman 'yan bindigar," in ji Adamu.
- Bayar da tsari da zai bayyana wa jama'a manufar gwamnati: Masanin ya kuma ce ya kamata gwamnati ta bayyana wa jama'a yadda ake tafiyar da lamuran tsaro da kuma manufofin da take son cimma. "Gwamnati ta fitar da tsari wanda zai bai wa 'yan ƙasa fahimtar abubuwan da ake ciki, me ake yi, ita gwamnati ne ke goyon bayan sulhu da ƴan bindiga kuma me take son ta cimma," in ji shi.
- Karfafa tsaro a fadin yankuna: Kabiru Adamu ya kara da cewa ya kamata gwamnati ta karfafa jami'an tsaro a yankunan da abin ya shafa tare da bai wa mutanen da hare-hare ya shafa ɗauki da diyya domin su sami abin dogaro.










