Abin da muka sani kan fashewar bama-bamai a Maiduguri

Bayanai na ƙara fitowa kan fashewar wasu abubuwa da ake zaton bama-bamai ne a sassan birnin Maiduguri na jihar Borno, lamarin da ya jefa al'umma cikin fargaba.
Tashin abubuwan fashewar ya faru ne kusan a lokaci guda a yammacin ranar Litinin, inda ya tashi a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri da babbar kasuwar 'Monday Market' da kuma ofishin aikewa da saƙonni ko gidan waya.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin 16 ga watan Maris, ƙasa da sa'oi 15 bayan wasu da ake zaton mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari a cibiyoyin sojin Najeriya a Ajari da Baga da kuma Damboa.
Wani da lamarin ya faru a kusa da wajen da suka yi buɗa-baki ya shaida wa BBC cewa ''Mun sha ruwa muna zaune, sai kawai jin ƙara muka yi, sai kuma ga mutane suna gudu wasu cikin jini, to muma dai daga nan sai kowa ya kama gaban shi. Da idona dai na ga mutanen da suka jikkata babu adadi.''
Shi ma wani da ya shaida yadda lamarin ya faru ya ce ya ga mutane cikin halin tashin saboda abin da ya faru, ya ce ''Waɗanda na gansu sun zo an wuce da su mutane biyra ne, akwai mace ɗaya da wani yaro, sai kuma wasu maza guda biyu. Inda bom ɗin ya tashi, a daidai wajen inda ake lodi ne na Unguwanni, sai dai a nan inda Bom ɗin ya tashi, akwai masu fenti, akwai masu baro waɗanda suke saida kayayyaki haka, duk ya ritsa da su.''
Can kuwa a kusa da asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri, wani ganau ya ce an samu jikkatar mutane kuma da asarar rayuka.
Ya ce ''Na ga mutumi uku dai wanda an rufe su wanda kamar basu da rai, sai kuma waɗanda aka shigo da su a jikkace dai duk a cikin jini da mata da maza da kuma yara ƙanana haka.
Sai dai wata sanarwa daga rundunar ƴansandan jihar ta Borno mai ɗauke da sa hannun kakakinta ASP Nahum Daso ta tabbatar da faruwa lamarin amma bata bayar da wani bayani game da ainihin abun da ya faru ba.
Ta dai jaddada cewa jamai'an tsaro da na bayar da agajin gaggawa a wajen da lamnarin ya faru, sannan ta yi kira ga al'ummar jihar da su kwantar da hankulansu, tare da ƙauracewa wurin da lamarin ya faru har zuwa lokacin da za su kammala tattara bayanai.
Zulum ya yi Allah-wadai da harin
Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, ya yi Allah-wadai da harin.
Zulum, wanda yanzu haka yake a Saudiyya domin aikin Umrah, ya bayyana harin a matsayin wani mummunan abu da aka ƙaddamar kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, duk da cewa ana cikin watan Ramadan.
Sanarwar da kakakin gwamnan jihar Borno, Dauda Iliya ya fitar, ta ce gwamnan ya yi kiran a ƙara jami'an tsaro a wuraren ibada.
Ya ce "Ina matuƙar baƙin cikin fashewar abubuwa a sassan Maiduguri, a ranar Litinin''
"Ina ta'aziyya ga dukkan iyalai da ƴan uwan mutanen da lamarin ya ritsa da su.''
Gwamnan ya ce yanzu haka sojoji da sauran jami'an tsaro na ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cikakken tsaro a kan jirgin, kuma a lokaci da dama kitsen da yaran ka ke lafta mani.












