Me ziyarar Tinubu zuwa Fadar Birtaniya ta ƙunsa?

Sarki Charles III da Shugaba Tinubu

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A yau ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kama hanya tare da mai ɗakinsa zuwa Birtaniya domin amsa gayyatar ziyarar aiki da fadar Birtaniya ta yi masa.

Wanan ce ziyara ta farko cikin shekara 37 da wani shugaban Najeriya ke kai wa fadar bisa gayyatar sarki.

Sarki Charles III na Birtaniya da mai ɗakinsa Saurauniya Camilla ne za su tarbi Shugaban na Najeriya a lokacin ziyarar da aka shirya manyan liyafa.

Ziyarar aiki da shugaban ƙasa ke kaiwa fadar Buckingham ta kasance wata muhimmiyar hanyar inganta alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashe da Birtaniya, inda ake tattauna hanyoyin cin gajiyar juna.

Rabon da shugaban Najeriya ya kai irin wannan ziyara Birtaniya tun a 1989, lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya ziyarci mariganya Sarauniya Elizabeth II, inda ya shafe kwanaki huɗu.

Yaya ziyarar za ta kasance?

Shugaba Tinubu da mai ɗakinsa za su isa Birtaniya a yau Talata 17 ga watan Maris na 2026, inda za su sauka a filin jirgin saman a Landan Stansted.

Mataimakin Laftanar na Essex ne zai tarbe su a madadin Sarki, da kuam jakadan Najeriya a Birtaniya, Ambassador Mohammed Maidugu, kamar yadda aka tsara

Sai a ranar Laraba ne 18 ga watan Maris, lokacin da Yarima mai jiran gado, Yarima William da da mai ɗakinsa , za su tarbi shugaban Najeriyar da mai ɗakinsa, a madadin sarki a otal din Farimont da ke Windsor.

Daga nan za su tafi da Shugaba Tinubu zuwa fadar sarki ta kan babban titin Datchet, inda za aka shirya musu liyafar maraba.

dawaki

Asalin hoton, Getty Images

Abubuwan da aka shirya musu

Bayan sun isa fadar, Sarki Charless III tare da mai ,ɗakinsa Sarauniya Camilla za su yi musu maraba a hukumance, daga nan za a kunna wutar girmamawa a fadar Windsor da kuma benen Landon da aka fi sani da 'London Tower'.

Za a gabatar da su a fadar, sannan tsaron lafiyar Sarki Charles za su yi gaisuwar ban girma, daga nan sai a kunna taken Najeriya.

Bayan haka shugaban na Najeriya da mai ɗakin nasa za su shiga cikin keken dawaki tare da Sarkin da mai ɗakinsa domin yin kilisa Fadar Windsor.

Keken dawaki

Asalin hoton, Getty Images

Za a yi wa shugabannin faretin ban girma a lokacin kilisar, inda za a riƙa kaɗa ganguna da busa kakaki irin na alfarma.

A lokacin faretin sioji, za a kunna taken ƙasashen Najeriy da na Birtaniya.

Daga Shugaba Tinubu da Sarki Charles za su zagaya zaratan sojojin domin duba faretin, su koma sai dakarun su ci gaba da baje-kolinsu na fareti, kafin a ƙarƙare.

Bayan nan can da yamma Shugaba Tinubu da mai ɗakinsa Remi za su je kallon baje-kolin abubuwan tarihi masu alaƙa da Najeriya a wani ɗakin adana kayan tarihi na fadar Birtaniyan.

Fadar sarki

Asalin hoton, Getty Images

Bayan haka kuma shugaban da matarsa za su kai ziyara maƙabartar St George da ke Fadar Windsor domin ajiye furanni a kabarin Sarauniya Elizabeth II a matsayin girmamawa.

Da daddare kuma akwai liyafar cin abincin dare da Fadar Sarki Charles III ta shirya wa Shugaba Tinubu da Remi.

A farko liyafar an tsara Shugaba Tinubu da Sarki Charles za su gabata da jawabai.

Remi Tinubu za ta gabatar da jawabi

Tinubu

Asalin hoton, @SenRemiTinubu/X

A ranar Alhamis 19 ga watan Maris da safe, Shugaban da mai ɗakin nasa za su yi wa Sarki Charles III da mai ɗakinsa bankwana a fadar Widsor, kafin su wuce zuwa babban ɗakin tarihi na Westminster Abbey, inda Shugaba Tinubu kai ziyara manyan ƙaburburan tsoffin sarakunan Birtaniya.

Bayan kammalawa da fada, Tinubu zai nufi Downing Street - ofoshin firaminsitan Birtaniya, Keir Starmer.

Ana sa ran shugabannin biyu za su yi tattaunawar da ta shafi harkokin diplomasiyya.

Yayin da ita kuma remi Tinubu za ta nufi babban cocin Lambeth - gidan Archbishop na Canterbury, shugaban cocin Ingila.

Ana sa ran za ta jagoranci gudanar da wasu addu'o'i a cocin.

Shugaba Tinubu da uwar gidan tas za su sake haɗuwa da juna domin halartar wata liyafar da ƴan Najeriya mazauna Birtaniya.

Ana sa ran Tinubu da mai ɗakin tasa za su bar Birtaniya da maraicen ranar Alhamis 19 ga watan n Maris.