Wane ne Ali Larijani, sakataren tsaron Iran da Isra'ila ta kashe?

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Talata, 17 ga watan Fabrairu ne kafafen watsa labaran Isra'ila suka ruwaito cewa dakarun Isra'ilar sun kashe Sakataren Majalisar Tsaron ƙasar Iran, Ali Larijani bayan kai masa hari tare da ɗansa a wani gida da "suke ɓoye".
Ministan tsaron Isra'ila, Israel Kartz ya ce "an kashe" Larijani sannan kuma Firaministan Isra'ila ya bai wa dakarunsa umarnin ci gaba da farautar sauran jagororin ƙasar ta Iran.
Wane ne Ali Larijani?

Asalin hoton, Getty Images
Sunansa Ali Ardeshir Larijani kuma an haife shi ne a shekarar 1953 a garin Najaf. Sunan mahaifinsa Ayatollah Hashem Amoli Larijani.
Ali Larijani shi ne sakataren Majalisar Tsaron ƙasar Iran kuma masana na ganin shi ne ke bayar da umarnin kai hare-haren martani a kan ƙasar Isra'ila da muradan Amurka da ke ƙasashen Gabas ta Tsakiya, tun bayan rasuwar jagoran addinin ƙasar ta Iran, Ayatollah Ali Kahamenei.
A watan Agustan 2025 ne shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian ya naɗa Larijani a matsayin sakataren majalisar kuma wakilin jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Kafin nan Ali Larijani ya zama kakakin majalisar dokokin Iran har tsawon shekaru 12 wato daga watan Maris na 2008 zuwa watan Mayu 2020.
Kafin zama kakakin majalisar, Larijani ya kasance mai shiga tsakanin kan batun nukiliyar Iran tsakanin 2005 zuwa 2007.
Larijani ne tsohon mai shiga tsakani na Iran kan batun nukiliya sannan kuma aminin marigayi Ayatollah Ali Khamenei.
Muƙaman da Larijani ya riƙe

Asalin hoton, Getty Images
- 1989 - 1992: Mataimakin shugaban haɗakar rundunar IRGC
- 1992 - 1993: Ministan Addinin Musulunci da Al'adu
- 1993 - 2004: Shugaban ƙungiyar kafafen watsa labaran Iran
- 2005 - 2007: Sakataren Mjalisar Tsaro
- 2008 - 2020: Wakili kuma kakaki a Majalisar Tuntuɓa ta Musulunci
- 2020 zuwa yau: Mai bai wa jaoran addini shawara kuma cikakken mamba a Majalisar raya al'adu ta Iran
- 2005: Dantakarar shugabancin ƙasar Iran inda ya zo na biyar a cikin mutum shida.
Mutumin da ke takalar Trump

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka hangi Ali Larijani a cikin jerin gwanon masu nuna goyon bayan ƴancin Falasɗinawa da ake wa laƙabi da Ranar Quds da aka yi a faɗin ƙasar Iran a ranar.
Bayyanar Larijani da shugaban ƙasar, Masoud Pezeshkian da ministan harkokin waje, Abbas Aragchi a jerin zanga-zangar sun musanta iƙrarin da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi cewa jagororin ƙasar Iran suna gudu su ɓuya saboda tsoron hare-haren.
Kafin nan kuma Larijani ya tsokani Donald Trump inda ya wallafa a shafinsa na X cewa " Trump ya ce yana son samun nasara cikin sauƙi. To amma ya sani cewa fara yaƙi abu ne mai saukƙi amma kuma ba za a yi nasara ba ta hanyar wallafe-wallafe a kafafen sada zumunta ba.
"Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba har sai mun sa ka yi da-na-sanin kuskuren da ka yi."
A wani saƙon na daban kuma da ya wallafa a ranar 10 ga watan Maris, Larijani ya ce Iran ba ta tsoron barazanar Trump inda ya ƙara da cewa "hatta waɗanda suka fi ka ƙarfi ba su iya kawar da ƙasar Iran ba."
"Kai ma ka bi a hankali, idan ba haka ba za mu kawar da kai," in ji Larijani.










